APC ta kara karfi a Kwara bayan Ahmed Aluko ya bar PDP

APC ta kara karfi a Kwara bayan Ahmed Aluko ya bar PDP

Mun samu labari cewa wani jigo a Jam’iyyar PDP a Jihar Kwara Ahmed Yinka Aluko ya sauya-sheka zuwa Jam’iyyar APC. Aluko ya fice ne ana wajen babban taron da Jam’iyyar PDP ta shirya jiya.

Babban Jam’iyyar adawa watau The Peoples Democratic Party ta rasa daya daga cikin manyan ‘Ya ‘yan ta Ahmed Yinka Aluko wanda ya tattara ya koma APC. Ahmed Aluko yayi takarar Mataimakin Gwamna a Jam'iyyar PDP a 2015.

APC ta kara karfi a Kwara bayan Ahmed Aluko ya bar Jam’iyyar

Jigon Jam’iyyar PDP ya fice daga Jam’iyyar wajen wani taro ya koma APC

A halin yanzu Ahmed Aluko ne kadai ke wakiltar Jihar Kwara a Majalisar zartarwa na Jam’iyyar PDP. A taron na NEC da aka shirya a makon nan ne babban ‘Dan siyasar ya fice daga Jam’iyyar bayan ta koma hannun Bukola Saraki.

KU KARANTA: Yanzu ba Jam'iyya ake bi illa cancanta - Shugaba Buhari

Yanzu dai Jam’iyyar ta APC mai mulki ta kara karfi a Jihar Kwara bayan da Ahmed Aluko ya bar Jam’iyyar. Aluko ya taba zama mai ba Gwamnatin Kwara shawara kan harkokin tsaro. ‘Dan siyasar ya bar PDP ne domin ba zai iya aiki da Saraki ba.

Kwanan nan ne Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da Gwamnan Jihar Kwara Abdulfatahi Ahmad da Shugabannin kakanan Hukumomi da kuma ‘Yan Majalisar su ka bar APC. Aluko yace ba a girmama irin su da su ka dade a PDP ba.

Bayan jin cewa Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki ya fice daga APC ya koma PDP ne Gwamnan Imo Rochas Okorocha yayi magana bayan jin wannan labari inda ya bayyana cewa sauyin shekar ba za ta canza komai ba a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel