Allah sarki: Za a maido wadanda ‘Yan Boko Haram su ka sace a 2016 gidajen su

Allah sarki: Za a maido wadanda ‘Yan Boko Haram su ka sace a 2016 gidajen su

- Wasu da Boko Haram su ka sace shekaru da dama za su dawo gida

- Rundunar Sojojin Najeriya ne su ka kubuto wadannan Bayin Allah

- An kuma karbe wasu makamai daga hannun ‘Yan ta’addan a Dikwa

Allah sarki: Za a maido wadanda ‘Yan Boko Haram su ka sace a 2016 gidajen su

Sojoji sun ceto wasu yara daga hannun ‘Yan Boko Haram

Wani labari mai dadi ya kai gare mu cewa Rundunar Sojin Najeriya sun ceto wasu Bayin Allah da ‘Yan Boko Haram su ka sace fiye da shekaru 2 da su ka wuce a Garin Ngafure da ke cikin Karamar Hukumar Dikwa a can Jihar Borno.

KU KARANTA: 'Yan siyasa ke haddasa rikicin siyasa a Najeriya - Minista

Yanzu haka Sojojin Najeriya na Bataliyar Operation LAFIYA DOLE sun ceto wasu yara har 4 da ‘Yan ta’addan Boko Haram su kayi awon-gaba da su kwanakin baya, kuma za a maida su gaban Iyayen su bayan an fitar da tsammani.

Rundunar Sojojin na Najeriya na 22 sun kai wa ‘Yan ta’addan Boko Haram hari a Garin Maima da ke cikin Garin Ngala inda su ka ceto yara ‘yan mata 2 da kuma wasu maza 2. Yanzu haka dai yaran su na karkashin kular likitoci.

Da zarar an duba yaran a asibiti za a mika su wajen iyayen su da aka raba su da su shekaru 2 da su ka wuce. Sojojin sun kuma yi nasara karbe makamai da su ka hada da bam a hannun ‘Yan ta’addan inji Darektan yada labarai na gidan Soji.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel