Zargin mu da ake yi a fashin Offa ne ya tursasa mu barin APC - Ahmed

Zargin mu da ake yi a fashin Offa ne ya tursasa mu barin APC - Ahmed

Gwmnan jihar Kwara, Alhaji Abdulfatah Ahmed, yace danganta shi da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da akayi da fashin Offa na daya daga cikin dalilan da yasa su barin jam’iyyar All Progressives Congress zuwa Peoples Democratic Party.

Gwamnan ya zargi gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari da tozarta shugabannin jam’iyyar a Kwara.

Ya kara da cewa jam’iyyar APC ta gaza cika burukan mutanen jihar.

Zargin mu da ake yi a fashin Offa ne ya tursasa mu barin APC - Ahmed

Zargin mu da ake yi a fashin Offa ne ya tursasa mu barin APC - Ahmed

Yayi korafin cewa ana nunawa jihar Kwara wariya wajen shirya abubuwa a gwamnatin Buhari.

KU KARANTA KUMA: Karin matsayi: An nada Saraki a matsayin uban jam’iyyar PDP na kasa

Ahmed yayi maganan ne a lokacin da wasu mata da matasa karkashin kungiyar Kwara Agenda suka shirya masa gangami a manyan hanyoyin jihar a ranar Alhamis, 2 ga watan Agusta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel