Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya isa Landan

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya isa Landan

Labarin da ke shigowa yanzun nan na nuna cewa jirgin shugaba Muhammadu Buhari, ya sauka lafiya a kasar Birtaniya domin hutun kwanaki goma, a birnin Landan.

Jirgin Shugaba Buhari Eagle 001 ya tashi a babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke birnin tarayya Abuja domin zuwa birnin Landan da asuban yau Juma'a, 3 ga watan Agusta 2018.

A bayansa, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne zai kasance mukaddashin shugaban kasa kuma yanada karfin zartar da duk wani hukuncin shugaban kasa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya aika wasikar haka ga majalisan dokokin tarayya yayinda ya nuna niyyarsa na daukan hutu da shari'a ta tanadar masa.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya bukaci a dakatar da yakin neman zabensa

Jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party PDP ta sakin jawabin cewa shugaba Buhari ya daura niyyan tafiya ne saboda ana shirin amfani da jami'an tsaro wajen cin mutuncin yan majalisan da suka sauya sheka daga jam'iyyar APC.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel