Kalli yawan kuri'un da ake saran Buhari zai samu a Kudancin Najeriya

Kalli yawan kuri'un da ake saran Buhari zai samu a Kudancin Najeriya

Da alama dai mutanen yankin kudu maso gabashin Najeriya sun dadin mulkin shugaba Buhari, inda hasashe ya nuna cewar shugaban kasar zai iya samun kusan sama da kashi 73 cikin dari na kuri'un yankin

Kalli yawan kuri'un da ake saran Buhari zai samu a Kudancin Najeriya

Kalli yawan kuri'un da ake saran Buhari zai samu a Kudancin Najeriya

A ranar Alhamis ne tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Kalu, yace shugaban kasa Muhammadu Buhari zai samu kashi 73 cikin dari na kuri'un yankin kudu maso gabas a zaben 2019 dake zuwa, domin nuna godiyar aiyukan da yayi wa yankin.

Kalu ya fadi hakan ne a taron zababbun yan jam'iyyar APC na gunduma, karamar hukuma da jiha da akayi a Igbere, karamar hukumar Bende dake jihar Abia.

DUBA WANNAN: Takardar bogi: SERAP ta baiwa hukumar NYSC kwanaki 7 ta gabatar da shaida akan Kemi Adeosun

Yace Buhari yayi wa yankin abinda shugabannin da suka gabata wanda ya hada da Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan basuyi musu ba.

Kalu ya lissafo gyaran babban titin Enugu zuwa Fatakwal, Enugu zuwa Onitsha da kuma aikin gadar Niger a cikin manyan aiyuka da Buhari yayi wa kudu maso gabas din.

Tsohon gwamnan yace babban kalubalen da yankin ke fuskanta dama sune tituna da kuma gadar Niger. Ya nuna farin cikin shi da Buhari ya share musu kukan su.

Kalu ya kara tabbatar da cewa APC zata samu gagarumar nasara a jihar Abia.

Bazamu bar kowa yayi mana magudin zabe ba domin mun shirya tsaf don zaben 2019. Inji Kalu.

Ya bukaci yan jam'iyyar da kada su tsorata da mutanen dake ta barin jam'iyyar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel