Obasanjo ne babbar matsalar Najeriya - Soyinka, Falana

Obasanjo ne babbar matsalar Najeriya - Soyinka, Falana

- An bayyana tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo a matsayin wanda yaki bin dokar kotin koli

- Shahararren marubucin nan Wale Soyinka shida Babban Lauyan nan na kare hakkin Dan Adam Femi Falana, sun bayyana shi a matsayin babbar matsala a kasar nan

Obasanjo ne babbar matsalar Najeriya - Soyinka, Falana

Obasanjo ne babbar matsalar Najeriya - Soyinka, Falana

A jiya ne shahararren Farfesan nan kuma marubuci, Wole Soyinka da kuma lauyan nan da yake kokarin kare hakkin dan adam Femi Fulana suka kaiwa tsohon Shugaban kasar Nageriya Olusegun Obasanjo farmaki inda suka bayyana shi a matsayin wani bangare na matsalar kasar nan, ba kamar yanda yake kiran kansa ba a matsayin wanda yake so ya ceto Najeriya daga halin da take ciki.

Soyinka da Falana sunyi wannan tattaunawa ne tare da shugaban marubuta na kasa Sam Omatseye a yayin kaddamar da wani littafi a jihar Legas.

DUBA WANNAN: 'Yan Najeriya sun daina siyasar jam'iyya yanzu, cancanta suke bi - Garba Shehu

Soyinka yace ya zame masa dole ya rubuta littafin saboda wasu abubuwa daya gani a cikin littafin Obasanjo mai suna "My Watch ".

" Wannan mutumin bazai taba daukar wani nauyin wani abu ba, sannan abun dana samu ba abun karbuwa bane ga mutumin da yake ikirarin shi mai tallafa wa kasa ne."

Falana ya kara bayyana Obasanjo matsayin wanda yakibin umarnin kasa.

"Tun lokacin da aka hada yankin Kudu da Arewa wanda akayi a shekarar 1914 ba wata gwamnati data bi dasu ba tare da cutarwa ba, yanda gwamnatin Obasanjo ta tafiyar da sha'anin kotun a lokacin da aka samu sabani tsakanin jihar Legas da kuma gwamnatin tarayya, inda kotun ta bada umarnin da a biya kudin amma Obasanjo yaki," inji Falana.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel