Karin matsayi: An nada Saraki a matsayin uban jam’iyyar PDP na kasa

Karin matsayi: An nada Saraki a matsayin uban jam’iyyar PDP na kasa

An nada shugaban majalisar dattawa, Bukola Sraki a matsayin uban jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP na kasa a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka gudanar a ranar Alhamis, 2 ga watan Agusta.

A matsayinsa na wadda ke rike da mukami mafi girma a jam’iyyar a yanzu, Saraki zai maye gurbin mataimakinsa, Sanata Ike Ekweremadu, wadda ke rike da mukamin har zuwa lokacin da Saraki da sauyan mambobin APC suka sauya sheka zuwa PDP.

Karin matsayi: An nada Saraki a matsayin uban jam’iyyar PDP na kasa

Karin matsayi: An nada Saraki a matsayin uban jam’iyyar PDP na kasa

Zuwan Saraki ya haifar da tarin ihu yayinda ya samu jagorancin shugaban jam’iyyar PDP, Uche Secondus da sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa dakin taron.

KU KARANTA KUMA: Sauya shekar Saraki, Tambuwal da sauransu ya sabama kundin tsarin mulki - Falana

Saraki, Rabiu Kwankwaso, gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal da gwamnan jihar Benue Samuel Ortom duk sun halarci taron.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel