Shugaba Buhari ya shahara wajen yawon fita neman lafiya - Ben Bruce

Shugaba Buhari ya shahara wajen yawon fita neman lafiya - Ben Bruce

Wani dan majalisa mai wakiltar mazabar Jihar Bayelsa ta Gabas, Sanata Ben Murray-Bruce, ya yabawa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, dangane da neman lafiyar sa da ya rika yi cikin kasar sa ta gado sabanin yadda shugaba Muhammadu Buhari ya shara akan yawon neman lafiya a kasashen ketare.

Cikin wani jirwaye mai kama da wanka da sanatan ya rubuta kan shafin na sada zumunta a ranar Alhamis din da ta gabata, Ben Bruce ya bayyana shugaban kasa a matsayin tataccen mashahuri wajen fita yawon neman lafiya a kasashen ketare.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, Sanatan ya bayyana ra'ayin sa ne bayan da tsohon shugaban kasa Obasanjo ya ziyarci jihar Bayelsa domin duban lafiyar sa kwanaki kadan da suka gabata.

Shugaba Buhari ya shahara wajen yawon fita neman lafiya - Ben Bruce

Shugaba Buhari ya shahara wajen yawon fita neman lafiya - Ben Bruce

Yake cewa, wannan shi yake tabbatar da amincin gami da soyayyar kasar Najeriya dake kunshe cikin zuciyar tsohon shugaban kasar. Sai dai ya bayyana cewa, shugaba Buhari yana daya daga mutane mafi shahara ta fuskar neman lafiya a birnin Landan.

Legit.ng ta fahimci cewa, a ranar yau ta Juma'a ne shugaba Buhari ya fara hutun sa na kwanaki goma, inda ya shilla birnin Landan na kasar Birtaniya domin ganawa da likitocin sa kamar yadda ya saba.

KARANTA KUMA: Tumɓuke Buhari daga Kujerar sa ba abu ne mai sauƙi ba - Buba Galadima

A sanadiyar haka cikin wasu sakonni da sanatan ya bayyana a shafin sa na sada zumunta, ya fedewa gwamnatin shugaban Buhari da jam'iyyar sa ta APC Biri har wutsiya musamman a bangaren mulkin kama karya.

Rahotanni sun bayyana cewa, Sanatan ya kuma bayyana takaicin sa dangane da yadda gwamnatin shugaba Buhari ke ribatar kujerar mulki wajen amfani da hukumomin tsaro domin cin zarafin 'yan adawar sa na siyasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel