Sauya shekar Saraki, Tambuwal da sauransu ya sabama kundin tsarin mulki - Falana

Sauya shekar Saraki, Tambuwal da sauransu ya sabama kundin tsarin mulki - Falana

Lauyan dake kare hakkin dan adam, Femi Falana, ya caccaki lamarin suya shekar shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki; Gwamna Aminu Tambuwal, takwaransa na Kwara, Abdulfatah Ahmed, daga jam’iyyar All Progressives Congress, APC, zuwa Peoples Democratic Party, PDP cewa ya sabama kundin tsarin mulki.

Hakan na zuwa ne a daidailokacin da lauyan kundin tsarin mulki kuma mai kare hakkin dan Adam, Cif Mike Ozekhome ya yi watsi da kiran da shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole yayi na cewa shugaban majalisar dattawa Saraki yayi murabus daga matsayinsa na shugaban majalisar bayan ya sauya sheka daga APC zuwa PDP.

Sauya shekar Saraki, Tambuwal da sauransu ya sabama kundin tsarin mulki - Falana

Sauya shekar Saraki, Tambuwal da sauransu ya sabama kundin tsarin mulki - Falana

Bayanin Falana na zuwa ne bayan Tambuwal da Saraki, Ahmed da wasu yan majalisa 23 a jihar sun sauya sheka daga APC zuwa PDP.

KU KARANTA KUMA: Matsalar tsaro a Najeriya: Karamin aikin yan siyasa ne – Inji Ministan Buhari

Da yake watsi da wannan shiri nasu na sauya sheka, Falana yace babu wani rikici a APC da ya bayar da damar sauya shekarsu daga jam’iyyar zuwa PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel