2019: Kwankwaso, Saraki, Tambuwal za su yi takatar Tikitin jam'iyyar PDP

2019: Kwankwaso, Saraki, Tambuwal za su yi takatar Tikitin jam'iyyar PDP

Mun samu rahoton cewa jam'iyyar adawa ta PDP, ta bayar da sahalewar ta kan wasu jiga-jigai uku na jam'iyyar da su nemi tikitin ta domin tsayawa takarar kujerar shugaban kasa a babban zabe na 2019.

Jam'iyyar ta bayar da amincewar neman tikitin ta kan tsohon gwamna kuma Sanatan jihar Kano ta tsakiya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, Shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki da kuma gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal.

Kazalika jam'iyyar da bayar da amincewar kan sauran mambobin jam'iyyar musamman wadanda suka shekar dawo cikin ta daga jam'iyyar APC akan su nemi tikitin takara kujerun siyasa daban-daban a kasar nan.

2019: Kwankwaso, Saraki, Tambuwal za su yi takatar Tikitin jam'iyyar PDP

2019: Kwankwaso, Saraki, Tambuwal za su yi takatar Tikitin jam'iyyar PDP

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito, kwanaki kadan da suka gabata Tambuwal, Kwankwaso da kuma Saraki, sun raba gari da jam'iyyar APC ne inda suka dawo jam'iyyar PDP musamman don samun tikitin takarar kujerar shugaban kasa.

KARANTA KUMA: Sauyin sheƙa tsarkaka ce ta jam'iyyar APC - Gwamna Bello

A yayin taron shugabannin jam'iyyar karo na 81 da aka gudanar cikin Birnin Abuja a ranar Alhamis din da ta gabata, shugaban jam'iyyar Prince Uche Secondus ya bayyana cewa, wadanda suka dawo jam'iyyar suna da hakkoki daidai da wadanda suka dade cikin jam'iyyar.

Rahotanni sun bayyana cewa, dukkanin masu hankoron kujerar shugaban kasa karkashin inuwa ta jam'iyyar sun halarci wannan taro in banda tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel