Matsalar tsaro a Najeriya: Karamin aikin yan siyasa ne – Inji Ministan Buhari

Matsalar tsaro a Najeriya: Karamin aikin yan siyasa ne – Inji Ministan Buhari

Ministan harkokin cikin gida, Abdulrahman Dambazau ya bayyana cewa yan siyasa na da hannu dumu dumu wajen rura matsalolin tsaro da ake fama dasu a Najeriya, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Dambazau ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, 2 ga watan Yuli yayin wata ganawar gaggawa akan matsalolin tsaro da aka yi a babban birnin tarayya Abuja, inda yace: “Siyasar kabilanci na taimakawa wajen rura rikice rikice a Najeriya.

KU KARANTA: Ba zan cuceku ba, ba kuma zan yarda wani ya cuceku ba – Buhari

“Yan siyasa na amfani da bambamce bambamcen kabilanci wajen sauya ma yan kabilunsu tunani, wanda hakan ke kawo rarrabuwar kai da kuma ingiza jama’a wajen yin bara’a ga gwamnatin. Matsalar tsaro a Najeriya ba irin wanda aka saba dasu bane.

Matsalar tsaro a Najeriya: Karamin aikin yan siyasa ne – Inji Ministan Buhari

Rikici

“Muna fama da irin namu ta’addancin, zagon kasa da kuma rikicin akan bambamcin addini da kabilanci, akwai alamomi karfafa dake nuni da cewa akwia siyasa a tashin tashinan da muke fama dasu a kasar nan, yayin da ake kitsa mana wasu daga kasashen waje.” Inji Dambazau.

Sai dai ministan ya bayyana ma mahalarta taron da suka hada da manyan jami’an tsaron kasar nan cewa ya zama wajibi dukkanin hukumomin tsaro dake Najeriya su tabbatar da tsare tsaren dakile rikici, shawo kansa da kuma hana aukuwarsa.

Daga karshe, Damzabau ya bukaci hukumomin tsaro dasu tabbata suna hadin gwiwa a tsakaninsu tare da musayar bayanan sirri, wanda hakan zai taimaka matuka wajen magance matsalolin tsaro a Najeriya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel