Ka nemi afuwan El-Rufai da Buhari ko ka cigaba da zama a korarre – APC ga Shehu Sani

Ka nemi afuwan El-Rufai da Buhari ko ka cigaba da zama a korarre – APC ga Shehu Sani

Jam’iyyar APC reshen jihar Kaduna ta tabbatar da sallamar wakilin al’ummar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Shehu Sani daga cikinta, har sai ya nemi gafarar gwamnan jihar, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, inji rahoton The Cables.

Jam’iyyar ta lashi takobin ba zata daga ma Shehu Sani kafa ba har sai ya nemi baiwa El-Rufai tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari hakuri, kamar yadda shugaban APC a mazabar Tudun Wada, Ibrahim Togo ya bayyana.

KU KARANTA: Yan bindiga sun yi awon gaba da fitaccen Malamin Addinin Musulunci a jihar Kaduna

Ka nemi afuwan El-Rufai da Buhari ko ka cigaba da zama a korarre – APC ga Shehu Sani

El-Rufai da Shehu Sani

Togo yace wannan mataki da APC a mazaba ta dauka ya samu sahhalewar Uwar jam’iyyar a matakin jaha. “A gaskiya sharadin janye sallamar da aka yi ma Shehu Sani shi ne ya nemi afuwan jam’iyyar APC game da laifukan da ya tafka mata a baya, da cin mutuncin da ya yi ma shugaba Buhari.

“Haka zalika sai ya nemi afuwan jama’an jihar Kaduna da gwamnatin jihar kan rawar daya taka wajen hanata samun bashin dala miliyan 350 wanda bankin Duniya za ta bayar din cigaban jihar Kaduna.” Inji Togo.

Sai dai magoya bayan Sanatan sun yi watsi da wannan sallama, inda suka ce suna da tabbacin al’ummar Kaduna ta tsakiya za ta sake zabar Shehu Sani a karo na biyu don wakiltarsu a majalisar dattawa, a cewarsu ai sawum giwa ya take na rakumi.

Daga karshe shima shugaban jam’iyyar APC na jihar Kaduna, Emmanuel Jekada ya tabbatar da sallamar Shehu Sani.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel