Ba zan cuceku ba, ba kuma zan yarda wani ya cuceku ba – Buhari

Ba zan cuceku ba, ba kuma zan yarda wani ya cuceku ba – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar ma yan Najeriya cewa shi ba macuci bane, don haka ba zai cucesu ba, haka zalika ba zai zura idanu har ya bari wani daban ya cucesu ba, kamar yadda ya dauki alkawari inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Buhari ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, 2 ga watan Yuli a jihar Bauchi, yayinda ya halarci taron yakin neman zaben dan takarar APC na kujerar Sanatan Bauchi ta kudu, Lawal Yahaya Gumau.

KU KARANTA: Yan bindiga sun yi awon gaba da fitaccen Malamin Addinin Musulunci a jihar Kaduna

“Ina so ku sani cewa muna iya kokarinmu a mulkin wannan kasa da kuma al’ummar Najeriya, ina so ku sani bazan zalunceku ba, kuma b azan yarda wani ya zalunceku ba, burinmu shine mu inganta kasar ta bangaren tsaro, tattalin arziki, da yaki da cin hanci da rashawa, kuma ba zamu manta ba.” Inji Buhari.

Dayake tsokaci game da zaben Sanatan dake karatowa, Shugaba Buhari yace: “Nazo don na roki alfarma daga gareku,ku zabi Lawal Yahaya don ya zama Sanatan Bauchi ta kudu, mun san zai iya aikin da zaku tura shi, da fatan Allah ya bayyanar da munafukan cikinmu.”

A nasa jawabin, shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomole ya caccaki yan siyasar da suka fice daga jam’iyyar APC, suka koma PDP, inda yace mutanene dake adawa da shugaba Buhari, suna bakin ciki yana kokarin tabbatar da tsaro, inganta tattalin arziki da kuma kawar da cin hanci da rashawa.

Daga karshe dan takaran APC, Lawal Yahaya ya bayyana godiyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da samun daman halartar taron nasa, sa’annan yayi alkawarin ba zai baiwa jama’an Bauchi ta kudu kunya ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel