Dan Asara: Ya kashe mahaifinsa a masallaci a kan zargi

Dan Asara: Ya kashe mahaifinsa a masallaci a kan zargi

Wani mutum, Umaru Muhammadu Jauro Ori, ya hallaka mahaifinsa yayin da yake sallah a cikin wani masallaci.

Ori ya kashe mahaifin nasa ne bisa zargin cewar shine ke haddasa masa matsala a tsakaninsa da matar sa.

Yanzu haka an gurfanar da Ori gaban wata babbar kotun jihar Bauchi karkashin mai shari'a, Jastis Aliyu Baba Usman.

Kotun ta ji cewar Ori ya hallaka mahaifinsa, Umar Muhammed, ta hanyar sassara shi da adda lokacin da yake sallah a cikin wani masallaci dake garin Maltawa a karamar hukumar Misau ta jihar Bauchi.

Dan Asara: Ya kashe mahaifinsa a masallaci a kan zargi

Dan Asara: Ya kashe mahaifinsa a masallaci a kan zargi

Yayin gurfanar da shi gaban kotun a ranar Laraba, mai gabatar da kara, Hussein Ishaq Magaji, ya shaidawa kotu cewar Ori ya jiwa mahaifinsa ciwo a ka da kuma bayansa.

An garzaya da mahaifin nasa mai shekaru 70 babban asibitin garin Misau inda ya mutu sakamakon ciwukan da ya samu.

Wani kani ga Ori ya ce kafin ranar da ya hallaka mahaifin nasu sun shafe fiye da kwanaki biyu basu san inda yake ba.

Sannan ya kara da cewa ko bayan da ya kashe mahaifin nasu ya yi kokarin guduwa ne ba don matasa sun yi masa tara-tara sun kama shi ba.

DUBA WANNAN: Buhari ya shirya fita daga Najeriya ne bayan gama shirya tuggun tsige Saraki - PDP

Da yake amsa tambayoyin jami'an 'yan sanda, Ori ya bayyana cewar ya kashe mahaifin nasa ne saboda yana haddasa masa matsala a tsakaninsa da matar sa.

A cewar Ori ya yanke shawarar kashe mahaifin nasa ne bayan ya dawo gida ya tarar matar sa da suka haifi 'ya'ya uku bata nan, kuma da ya tambaya aka sanar da shi cewar mahaifin sa ne ya sallame ta daga gidan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel