Tumɓuke Buhari daga Kujerar sa ba abu ne mai sauƙi ba - Buba Galadima

Tumɓuke Buhari daga Kujerar sa ba abu ne mai sauƙi ba - Buba Galadima

Alhaji Buba Galadima, shugaban sabuwar kungiyar nan ta r-APC, yayi gargadin babban kalubalen dake tattare da tumɓuke shugaban kasa Muhammadu Buhari daga Kujerar sa a zaben 2019, da cewar ba zai tabbata ba cikin ruwan sanyi.

Cikin jawaban sa yayin bikin hadin kan jam'iyyu 39, Galadima ya gargadi kungiyar akan ta tashi tsaye tare da zage dantsen ta da cewar tumbuke tsohon Janar na soji daga kujerar mulki ba abu ne da zai tabbata ba cikin ruwan sanyi.

Shugaban na r-APC ya shaidawa kungiyar da jam'iyyar PDP ke jagoranta, akan su zama cikin shirin fuskantar duk wani cuzguni, kalaubalai gami da barazana yayin fafata wannan gagarumin yakin domin cimma manufar ta.

Tumɓuke Buhari daga Kujerar sa ba abu ne mai sauƙi ba - Buba Galadima

Tumɓuke Buhari daga Kujerar sa ba abu ne mai sauƙi ba - Buba Galadima
Source: Depositphotos

Yake cewa, "tumɓuke tsohon Janar daga kujerar mulki wani babban kalubale ne dake gaban da sai mun jajirce. Sai dai ko shakka babu za mu iya bakin kokarin mu wajen cimma nasara sakamakon 'yan Najeriya sama miliyan 200 dake dakon mu a zaben 2019."

Ya nemi wadanda ke kan shinge akan su gaggauta shigowa kungiyar hadin kan tare da yin kira ga hukumar zabe ta kasa watau INEC akan tabbatar da gaskiya gami da adalci yayin gudanar da zaben 2019.

KARANTA KUMA: Za a fara sayar da Tikitin Jiragen 'Kasa ta Yanar Gizo a watan Satumba - NRC

A cewar sa, yan Najeriya ba za su lamunci makamancin abinda ya wakana yayin zaben gwamna a jihar Ekiti, inda yace jam'iyyar APC ta tafka magudi iya son ranta.

A nasa jawaban, shugaban jam'iyyar PDP na kasa Prince Uche Secondus, ya bayyana damuwar sa da takaici dangane da yadda ake cin mutuncin shugabancin majalisar dattawa tare da mulkin kama karya da ake fuskanta a kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel