Sauyin sheƙa tsarkaka ce ta jam'iyyar APC - Gwamna Bello

Sauyin sheƙa tsarkaka ce ta jam'iyyar APC - Gwamna Bello

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana guguwar sauyin sheƙa ta ficewa daga jam'iyyar APC a matsayin wani salo na tsarkake ta daga baragurbi.

Gwamnan ya bayyana hakan ne da sanadin kakakin sa, Kingsley Fanwo, cikin birnin Lokoja a ranar Alhamis din da ta gabata da cewa a yanzu ne jam'iyyar za ta kara karfi bayar tankade gami da rairaye baragurbin ta.

Bello ya bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin mutum mai martaba, da yake samun girmamawa anan gida da kasashen ketare da ta zarce misali ko kwatance.

Sauyin sheƙa tsarkaka ce ta jam'iyyar APC - Gwamna Bello

Sauyin sheƙa tsarkaka ce ta jam'iyyar APC - Gwamna Bello

Yake cewa, an dasa jam'iyyar APC ne bisa tushe da akida ta kawo sauyi gami da manufa ta bayar da kariya ga bukatun talakawa cikin al'ummar kasar nan.

KARANTA KUMA: Arise: Dole ne Saraki da sauran 'Yan Majalisa da suka sauya sheka su sauka daga Kujerun su

Ya ci gaba da cewa, talakawan kasar nan za su tabbatar da nasarar shugaba Buhari a zaben 2019 sakamakon goyon bayan sa gami da tsarkakkiyar soyayyar sa dake zukatan su.

Bello ya kuma nemi mambobin jam'iyyar su ta APC akan ci gaba da goyon bayan shugaban Buhari domin kunyata abokanan adawar sa da makiya cikin kasar nan a zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel