Buhari bai da tamka a cikin ‘Yan siyasar kasar nan inji Kenneth Okonkwo

Buhari bai da tamka a cikin ‘Yan siyasar kasar nan inji Kenneth Okonkwo

- Wani ‘Dan fim ya nemi ‘Yan Ibo su goyi bayan Buhari

- Keneth Okonkwo yace Buhari mutum ne na Inyamurai

Wani ‘Dan wasan kwaikwayo Keneth Okonkwo yayi kira ga Jama’a su marawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zabe mai zuwa. Kenneth Okonkwo yace Shugaba Buhari na Inyamurai ne.

Kenneth Okonkwo mai shekaru 49 a Duniya yace ba za a taba samun wanda zai mulki kasar nan kamar Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Okonkwo dai ya na da niyyar fitowa takarar Gwamnan Jihar Enugu a zaben 2019.

KU KARANTA: An bayyana kutun-kutun din da Tambuwal ya shirya lokacin da Buhari yake jinya

Fitaccen ‘Dan wasan na Nollywood a wajen wani taron siyasa ya fadawa Inyamurai ‘Yan uwan sa cewa Shugaba Buhari mutum ne mai kaunar su a zuciya. ‘Dan wasan yace kuma Shugaba Buhari bai da tamka cikin ‘Yan siyasa.

Bayan nan kuma ‘Dan wasan yayi kira ga Jama’a da ke sha’awar yin gyara su shiga cikin harkar siyasa. ‘Dan wasan fim din yace shi dai ko ana ha-maza-ha mata yana tare da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a siyasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel