Wata sabuwa: Shugaba Kim na Koriya ta Arewa ya aikewa Shugaba Trump na Amurka da wasika

Wata sabuwa: Shugaba Kim na Koriya ta Arewa ya aikewa Shugaba Trump na Amurka da wasika

Fadar shugaban kasar Amurka ta White House a ranar Alhamis ta bayar da tabbacin samun wasika daga shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong Un zuwa takwaran sa na Amurka, Donald Trump.

Sai dai kuma kamar yadda muka samu daga majiyoyin mu, fadar shugaban kasar ta Amurka bata yi wani kwakkwaran karin haske ba game da abun da wasikar ta kunsa sai dai kawai suka ce wai tana cikin cigaban tattaunawar su da suka fara a watan Yuni da ya gabata.

Wata sabuwa: Shugaba Kim na Koriya ta Arewa ya aikewa Shugaba Trump na Amurka da wasika

Wata sabuwa: Shugaba Kim na Koriya ta Arewa ya aikewa Shugaba Trump na Amurka da wasika

KU KARANTA: Mafusatan matasa sun lalata allon kamfe din Buhari a Kano

Legit.ng ta samu cewa a watan na Yuni, shugabannin kasashen biyu sun yi wata ganawa mai cike da tarihi a kasar Singafo inda suka tattauna wasu muhimman batutuwa.

A wani labarin kuma, Da ranar yau ne dai manyan hafsohin tsaro a kasar Najeriya suka sa labule tare da shugaban kasa, Muhammadu Buhari a fadar sa dake Villa, babban birnin tarayya Abuja.

Sai dai bayan kammala taron nasu ne sai mai magana da yawun ministan tsaron kasar Mansur Dan-Ali ya fitar da sanarwar abunda aka tattauna a wajen raton na sirri.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel