Wani gwamnan PDP ya hana 'yan APC gudanar da taro a babban filin wasan jihar

Wani gwamnan PDP ya hana 'yan APC gudanar da taro a babban filin wasan jihar

Gwamnan jihar Ebonyi dake a kudancin Najeriya kuma jigo a jam'iyyar adawa ta PDP da kuma ke mulki a jihar mai suna Dabid Umahi, mun samu labarin cewa ya hana 'yan jam'iyya mai mulki a matakin tarayya yin anfani da babban filin wasan jihar wajen yin taro.

Sai dai da yake karin haske game da dalilin yin hakan, mai magana da yawun sa Cif Emmanuel Uzor ya bayyanawa 'yan jarida cewar ana aikin gyare-gyare ne ga filin wasan.

Wani gwamnan PDP ya hana 'yan APC gudanar da taro a babban filin wasan jihar

Wani gwamnan PDP ya hana 'yan APC gudanar da taro a babban filin wasan jihar
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Dole mu dage mu kori Buhari a 2019 - Sule Lamido

Legit.ng ta samu cewa daga nan ne kuma sai ya shawarci 'ya'yan jam'iyyar ta APC a jihar da su nemi wani wurin domin suyi taron su.

A wani labarin kuma, Hukumar makarantar koyar daa harkokin gudanarwa ta kasa watau Nigerian Institute of Management ta ce rabin 'yan kasar na fuskantar wariya da rashin adalci daga shugaba Buhari tun da ya hau mulki.

Hukumar dai ta cewa hakan na faruwa ne kuma saboda kin nada mata da ke zaman rabin 'yan Najeriya da yayi a cikin gwamnatin sa a madafun iko tun bayan darewar sa kan karagar mulki a shekarar 2015.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel