Tonon silili: Abin da ya sa Tambuwal ya fice daga APC Inji Fadar Shugaban kasa

Tonon silili: Abin da ya sa Tambuwal ya fice daga APC Inji Fadar Shugaban kasa

-` Tambuwal ya kudiri zama Shugaban kasa lokacin da Buhari yake jinya

-` Mai ba Buhari ce ta bayyana wannan bayan Gwamnan ya sauya sheka

Mai ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara a kafofin sadarwa ta bayyana kutun-kutun din da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya shirya lokacin da Shugaban kasa yake jinya kwanaki.

Tonon silili: Abin da ya sa Tambuwal ya fice daga APC Inji Fadar Shugaban kasa

Gwamna Sokoto ya ci burin zama Shugaban kasa kwanakin baya

Lauretta Onochie ta bayyana cewa Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal yayi kokarin karbe Gwamnati daga hannun Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Onochie tace Tambuwal din ya boyewa jama’a dalilin da ya sa ya bar APC.

Onochie tace Gwamna Aminu Tambuwal yayi aman sa ya lashe bayan komawar sa PDP duk da sukar Jam’iyyar da yayi a baya. Mai ba Shugaban kasar shawara ta shafin ta na Facebook tace Aminu Tambuwal din yayi karamar magana.

KU KARANTA:

Wannan Baiwar Allah da ke ba Shugaban kasa Buhari shawara tace a lokacin da Shugaba Buhari bai da lafiya, Gwamna Tambuwal yayi ta addu’a Ubangiji ya dauke ran Shugaban kasar domin ganin ya karasa wa’adin sa domin yana 'Dan Arewa.

Misis Onochie tace sam babu gaskiya a abin da Gwamnan na Sokoto ya fada bayan ya fice daga APC. Aminu Tambuwal yace daga cikin abin da ya sa ya koma Jam’iyyar PDP shi ne Gwamnatin Shugaba Buhari tayi watsi da Jihar Sokoto.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel