Siyasar Kano: Jami'an 'yan sanda sun cafke 'yan Kwankwasiyyar dake kona tsintsiya

Siyasar Kano: Jami'an 'yan sanda sun cafke 'yan Kwankwasiyyar dake kona tsintsiya

Wani rahoto da muke samu daga kafofin sadarwar zamani sun tabbatar mana da cewa jami'an 'yan sandan Najeriya a jihar Kano sun cika hannuwan su da wasu mabiya darikar kwankwasiyya a jihar.

Kamar dai yadda muka samu, yan sandan sun ce laifin da wadanda suka kama din da galibin su matasa ne shine na kona tsintsiya a bainar jama'a.

Siyasar Kano: Jami'an 'yan sanda sun cafke 'yan Kwankwasiyyar dake kona tsintsiya

Siyasar Kano: Jami'an 'yan sanda sun cafke 'yan Kwankwasiyyar dake kona tsintsiya

KU KARANTA: Yan Tijjaniyya a Adamawa sun fitar da sanarwa game da 'yan hakika

Legit.ng ta samu cewa 'yan sandan dai sun bayyana wannan a matsayin wani yunkuri na tada tarzoma da husuma musamman ma a wannan lokacin da siyasar jihar ta dauki sabon salo.

A wani labarin kuma, Da ranar yau ne dai manyan hafsohin tsaro a kasar Najeriya suka sa labule tare da shugaban kasa, Muhammadu Buhari a fadar sa dake Villa, babban birnin tarayya Abuja.

Sai dai bayan kammala taron nasu ne sai mai magana da yawun ministan tsaron kasar Mansur Dan-Ali ya fitar da sanarwar abunda aka tattauna a wajen raton na sirri.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel