Za a fara sayar da Tikitin Jiragen 'Kasa ta Yanar Gizo a watan Satumba - NRC

Za a fara sayar da Tikitin Jiragen 'Kasa ta Yanar Gizo a watan Satumba - NRC

Hukumar kula da harkokin layin dogo da jiragen kasa ta Najeriya, NRC (Nigeria Railway Corporation), ta yiwa 'yan Najeriya sabon albishir da garaɓasa ta fara sayar da tikitin jirage ta hanyar yanar gizo a watan Satumba.

Shugaban wannan hukuma, Mista Fidet Okhiria, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai cikin birnin tarayya a ranar Alhamis din da ta gabata.

Yake cewa, hukumar a halin yanzu tana matakin ƙarshe na kammala shirye-shiryen ta na samar da hanyar sayar da tikitin jiragen kasa ta yanar gizo cikin domin saukakawa mabukata.

Za a fara sayar da Tikitin Jiragen 'Kasa ta Yanar Gizo a watan Satumba - NRC

Za a fara sayar da Tikitin Jiragen 'Kasa ta Yanar Gizo a watan Satumba - NRC

Kamar yadda shafin jaridar Today Nigeria ya ruwaito, hukumar za kuma ta samar da sabuwar manhajar ta domin wayoyin salula na hannu da al'umma za su ribata su na daga kwance a gidajen su.

KARANTA KUMA: Riƙe mani albashi na ya saɓawa Shari'a - Olubadan

Legit.ng ta fahimci cewa, rahoton wannan garaɓasa ya bayyana a shafin sada zumunta na twitter da sanadin hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari akan harkokin sabuwar hanyar sadarwa, Bashir Ahmad, kamar haka:

Rahotanni sun bayyana cewa, hukumar ta kudiri wannan sabon salo domin kawo karshen wahalhalun sayen tikitin jirage da fasinjoji ke fuskanta kamar yadda Mista Okhira ya bayyana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel