Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya na shirin kara alawus din yan bautar kasa

Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya na shirin kara alawus din yan bautar kasa

Gwamnatin tarayya ta fara tsare-tsaren sake duba da kara alawus din da ake bay an bautar kasa a kowani wata.

Darakto Janar na hukumar kula da harkokin yan bautar kasa, Birgediya Janar Suleiman Kazaure wadda ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja yayinda ya ziyarci sansanin yan bautar kasa na birnin tarayya dake Kubwa yace shirin ya samu wata wasika daga fadar shugaban kasa inda ministar kudi ke aiki akan lamarin.

Yace saboda haka yan bautar kasar su jajirce wajen yiwa kasarsu hidima ta hanyar yin ayyukan da ya kamata.

Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya na shirin kara alawus din yan bautar kasa

Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya na shirin kara alawus din yan bautar kasa

Ya kuma bukace su da su zamo masu lura da tsaro domin guje ma fadawa cikin matsala sannan su guji yawo cikin dare su kadai, da kuma halartan gidajen rawa na dare.

KU KARANTA KUMA: Yan siyasa masu rashawa ne ke makale da Buhari a APC har yanzu - Galadima

Haka zalika ya umurce su da zamo masu gujewa shigar banza da tafiye-tafiye marasa amfani.

Daga karshe ya umurce su da suyi amfani da damar shirin koyar da ayyukan hannu da ake gudanarwa wajen koyon sana’o’i don samarwa da kansu aiki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel