Da duminsa: Ina nan daram a APC ban fita ba – Mataimakin gwamnan Kano
Mataimakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar, ya musanta rahoton dake yawo a gari cewar ya fita daga jam’iyyar APC tare da komawa jam’iyyar PDP.
Mista Abubakar ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya aikewa gidan jaridar Premium Times ta hannun Abdulwahab Ahmad, mai taimaka masa a bangaren yada labarai.
A jiya ne kafafen yada labarai suka wallafa rahotannin cewar Farfesa Hafiz ya fita daga APC tare da komawa PDP, jam'iyyar da maigidansa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya koma a satin da ya wuce.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng