Zaben 2019: Aisha Alhassan na neman sake tsayawa takarar Gwamna

Zaben 2019: Aisha Alhassan na neman sake tsayawa takarar Gwamna

-` Ministar mata a Najeriya Alhassa za ta jarraba sa’a a zaben 2019

-` Kwanaki aka ji Ministar ta na yi wa Atiku mubaya’a game da 2019

-` Buhari dai yace yana taya ta addu’ar neman sa’a idan lokaci yayi

Mun samu labari cewa Hajiya Aisha J. Alhassan wanda ta na cikin Ministocin Gwamnatin Shugaba Buhari ta na neman sake tsayawa takarar Gwamnan Jihar Taraba a zabe mai zuwa da za ayi a 2019.

Zaben 2019: Amina Alhassan na neman sake tsayawa takarar Gwamna

Nan gaba Amina Alhassan za ta nemi Gwamnan Taraba

Aisha Jummai Alhassan wanda ta nemi Gwamna a Jihar Taraba a karkashin Jam’iyyar APC za ta sake neman kujerar a zaben 2019. Mun fahimci wannan ne ta wata takarda da Ministar ta aikawa Shugaban kasa Buhari.

KU KARANTA: Ashe Buhari yace Kwankwaso yayi takarar Shugaban Kasa a 2015

Ministar harkokin mata da cigaban al’umma Alhassan ta aikawa Shugaba Buhari takarda inda ta sanar da shi cewa za tayi takara a zabe mai zuwa. Shugaba Buhari tuni dai yayi mata fatan alheri da Allah ya bada sa’a.

Shugaban Kasa Buhari ya maidawa Ministar ta sa amsa inda yace yana yi mata fatan alheri kuma Gwamnatin sa za tayi kokari wajen ganin an yi zabe na adalci a 2019 sannan da ganin kuma Jami’an tsaro sun yi aikin su.

Kwanan nan ne wani Minista a Gwamnatin Buhari ya lashe zaben Gwamna da aka yi a Jihar Ekiti. Shugaban Kasar yace za su cigaba da marawa duk wanda Jam’iyyar APC ta tsaida takara a zabe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel