Arise: Dole ne Saraki da sauran 'Yan Majalisa da suka sauya sheka su sauka daga Kujerun su

Arise: Dole ne Saraki da sauran 'Yan Majalisa da suka sauya sheka su sauka daga Kujerun su

Wani tsohon dan majalisar dattawa, Sanata Ayo Arise, yayi kira ga shugabacin jam'iyyar APC akan ta fara shirye-shirye domin tabbatar da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da sauran 'yan majalisa da suka sauya sheka sun rasa kujerun su.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne Sanata Arise ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a birnin Ado-Ekiti na jihar Ekiti, inda ya jajirce akan sai Saraki ya rasa mukamin sa na shugaban majalisar dattawa tare da rasa kujerar sa ta Sanata da yake wakilcin jihar Kwara ta Tsakiya.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, Sanata Arise ya yi wannan kira ne ga shugabancin jam'iyyar APC sakamakon takaicin rashin dacewa na ficewar 'yan majalisar daga cikin ta.

Dole ne Saraki da sauran 'Yan Majalisa da suka sauya sheka su sauka daga Kujerun su - Sanata Ayo Arise

Dole ne Saraki da sauran 'Yan Majalisa da suka sauya sheka su sauka daga Kujerun su - Sanata Ayo Arise

Tsohon dan majalisar ya kuma bukaci hukumar zabe ta kasa watau INEC, akan ta fara shirye-shiryen gudanar da zaben maye gurbin kujerun 'yan majalisar da suka sauya sheka, inda ya ce ba bu wanda ya cancanci ci gaba da rike kujerar sa.

Ya shawarci jam'iyyar ta APC akan ta tunkari kotun kolu domin tsige Saraki, Kwankwaso da sauran 'yan majalisar tarayya a suka sauya sheka ta ficewa daga jam'iyyar.

KARANTA KUMA: Rayukan Mutane 5 sun salwanta cikin wani hargitsi a jihar Filato

Arise ya ci gaba da cewa, ba bu wanda cancanci ci gaba da zama a kujerar sa cikin dukkanin 'yan majalisar da suka sauya sheka, inda ya nemi hukumar zabe ta tabbata sun rasa wannan dama da nasaba da suke da ita.

Ya kara da cewa, akwai rashin ɗa'a gami da rashin dacewa akan masu rike da kujerun gwamnati su sauya shekar su ta jam'iyya sabanin wanda aka zabe su a kanta, inda ya nemi kundin tsarin mulkin kasa ya sake nazari kan wannan lamari domin kawo karshen sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel