Riƙe mani albashi na ya saɓawa Shari'a - Olubadan

Riƙe mani albashi na ya saɓawa Shari'a - Olubadan

Wani Basarake can birnin Ibadan dake jihar Oyo, Oba Saliu Akanmu Adetunji, ya koka dangane da yadda masu naɗin sarautar ta Olubadan suke riƙe albashin sa har na tsawon watanni 11 da a cewar sa hakan ya saɓawa tanadi na Shari'a.

Oba Adetunji ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da sanadin hadimin sa akan hulda da manema labarai, Adeola Oloko, inda ya ke cewa akwai tanadin doka da shari'a kan dukkanin masarautun dake karkashin kananan hukumomi 11 na jihar ba tare da ci da karfi ba.

A sanadiyar hakan ya sanya cikin tanadin sashe na 76 cikin dokokin kananan hukumomi na jihar Oyo, Adetunji ya nemi hakkin masarautar sa cikin wata rubutacciyar wasika dangane da yadda aka dakatar da riƙe maƙogwaron albashi da alawus na dukkanin ma'aikatan fadar sa.

Riƙe mani albashi na ya saɓawa Shari'a - Olubadan

Riƙe mani albashi na ya saɓawa Shari'a - Olubadan

Kazalika, Olubadan ya aika da wannan wasika zuwa ga lauyan kolu kuma kwamishinan shari'a na jihar, kwamishinan kananan hukumomi da al'amurran da suka shafi masarauta tare da shugabannin kananan hukumomi na jihar domin neman a kawo ɗauki.

KARANTA KUMA: 2019: Ku zama cikin shirin yaki - Secondus ga masu sauya sheka zuwa PDP

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito, wannan Basarake ya aika da wasikar sa ne tun a ranar 16 ga watan Yulin da ta gabata zuwa ga shlkwatar kananan hukumomi na jihar inda suka dakatar da biyan albashin ma'aikatan fadar sa.

A yayin haka Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, rayukan mutane biyar sun salwanta yayin aukuwar wani hargitsi cikin jihar Filato a daren ranar Talatar da ta gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel