2019: Akwai gwamnonin PDP 4 dake yiwa APC aiki ta karkashin kasa - Kofa

2019: Akwai gwamnonin PDP 4 dake yiwa APC aiki ta karkashin kasa - Kofa

Abdulmumin Jibrin Kofa, dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomi Kiru da Bebeji a jihar Kano, ya yi ikirarin cewar akwai gwamnonin jam'iyyar PDP 4 dake aiki tare da jam'iyyar APC domin ta kai ga nasara a zaben 2019.

Duk da bai ambaci sunayen gwamnonin ba, Kofa ya bayyana cewar akwai yarjejeniya tsakaninsu da jam'iyyar APC.

Da yake ganawa da manema labarai a Abuja a jiya, Laraba, Kofa ya ce, "a halin yanzu akwai gwamnonin jam'iyyar PDP 4 zuwa 5 da aka kulla yarjejeniyar goyon bayan takarar shugaba Buhari da su a zaben shugaban kasa."

2019: An gano gwamnonin PDP 4 dake yiwa APC aiki ta karkashin kasa

Abdulmumin Jibrin Kofa

Sannan ya kara da cewa, "jam'iyyar APC ba ta girgiza ba saboda fitar wasu 'ya'yanta ba."

Kazalika ya kara da cewar APC na daukan matakan ganin cewar ta cigaba da juya siyasar jihohin da take da yawan magoya baya.

DUBA WANNAN: Tsige Bukola: Buhari ya gana da gwamnoni da Sanatocin APC

"Da a ce wani dan takarar APC ta tsayar ba shugaba Buhari ba, da sai na dan ji raina ya sosu saboda ficewar wasu 'ya'yan jam'iyyar amma yanzu bana jin ko dar a raina saboda shugaba Buhari ke yiwa APC takarar shugaban kasa.

"Duk masu sukar Buhari da canja sheka 'yan siyasa ne da basu da wasu jama'a, a saboda haka zaben 2019 zai kasance ne tsakanin 'yan Najeriya da wasu tsirarun 'yan siyasa masu son zuciya," in ji Kofa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel