Yan siyasa masu rashawa ne ke makale da Buhari a APC har yanzu - Galadima

Yan siyasa masu rashawa ne ke makale da Buhari a APC har yanzu - Galadima

Alhaji Buba Gadima, shugaban kungiyar sabuwar APC yace duk wadanda ke makale Buhari barayin yan siyasa ne.

Manyan jiga-jigan jam’iyyar All Progressive Party(APC) da dama sun sauya sheka inda suka koma babban jam’iyyar adawa ta PDP.

Bisa ga shafin jam’iyyar PDP na twitter, Galadima yace “Duk wadanda ke gudu zuwa @APCNigeria ko kuma suke cikin APC har yanzu ko suke tare da @MBuhari sunewadanda ked a hannu dumu-dumu cikin sata. Suna tsoron hukunci. Amma wadanda suka gudu daga @MBuhari da APC sune yan Najeriya masu gaskiya.”

A halin da ake ciki, Sabuwar gamayyar jam’iyyun siyasa 39 ta bayyana sakatariyarta na kasa a Abuja.

KU KARANTA KUMA: Kotun Kaduna ta sanya ranar 4 ga watan Oktoba don yanke hukunci kan belin Zakzaky

Jam’iyyar CUPP ta kansance jam’iyyar hadin gwiwa da ta tara jam’iyyun siyasa 39 ciki harda Peoples Democratic Party, Social Democratic Party da kuma Labour Party.

An kafa sabuwar jam’iyyar ne bisa kudirin kwace mulki daga hannun jam’iyyar All Progressives Congress mai mulki a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel