Yanzu yanzu: Yan bindiga sun yi awon gaba da fitaccen Malamin Addinin Musulunci a jihar Kaduna

Yanzu yanzu: Yan bindiga sun yi awon gaba da fitaccen Malamin Addinin Musulunci a jihar Kaduna

Wani rahoto da muka samu da dumi duminsa shi ne na wasu yan bindiga da suka yi awon gaba da fitaccen Malamin addinin Musunluncin nan dake zaune a jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Al-Garkawy tare da wasu dalibansa.

Jaridar Desert Herald ce ta ruwaito wannan labari, inda tace yan bindigan sun yi garkuwa da shehin Malamin tare da dalibansa ne a ranar Alhamis, 2 ga watan Agusta, a daidai lokacin da suka kai ziyara gonar makarantarsa dake gefen garin Kaduna.

KU KARANTA: Ramin karya kurarre ne: Manyan ayyukan gwamnatin tarayya guda 17 a jihar Sakkwato

Yanzu yanzu: Yan bindiga sun yi awon gaba da fitaccen Malamin Addinin Musulunci a jihar Kaduna

Garkawy

Majiyar Legit.ng ta ruwaito zuwa yanzu har yan bindigan sun nemi iyalan Malamin dasu biya kudin fansa kafin su saki Malamin da daliban nasa, sai dai ba’a bayyana adadin kudin da suka nema ba.

A yanzu haka hankulan jama’an unguwar da Malamin ke zaune, Unguwar Mu’azu dake cikin garin Kaduna ya tashi matuka, sakamakon suna amfana kwarai da gaske da Malam, ta karatuttukan da yake yi a kullum, da kuma makarantu da asibitocin da yake assasawa.

Duk da irin kokarin da gwamnatin tarayya take yi game da yaki da masu garkuwa da mutane a Najeriya, amma ayyukansu na cigaba da ta’azzara a yankin Arewa maso yamma, musamman ma a jihar Kaduna, lamarin da yafi shafar al’ummar garin Birnin Gwari.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel