Babban jigon PDP a Abuja ya sauya sheka zuwa APC da daruruwan mambobin jam’iyyar a Kuje

Babban jigon PDP a Abuja ya sauya sheka zuwa APC da daruruwan mambobin jam’iyyar a Kuje

Iliya Bulus, wani jigo a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) mai adawa da wasu mambobin jam’iyyar 482 sun sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a mazabar Gudun-Karya dake yankin Kuje, Abuja.

Daga cikin jigajigan jam’iyyar sun hada da Iliya Bulus, Sule Ayuba, Madam Aboki da Abdulrahman Zagabutu, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Godwin Poyi, shugaban APC babin Kuje, wadda ya tarbi masu sauya shekar, ya bayyana cewa sun dawo APC ne bisa ga nasarorin da jam’iyyar ta samu a yankin.

Babban jigon PDP a Abuja ya sauya sheka zuwa APC da daruruwan mambobin jam’iyyar a Kuje

Babban jigon PDP a Abuja ya sauya sheka zuwa APC da daruruwan mambobin jam’iyyar a Kuje

Yace sun yi farin ciki da tsoffin mambobin na PDP inda ya kara da cewa a koda yaushe za’a basu kula kamar na sauran mambobin jam’iyyar.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, Samuel Ortom na jihar Sokoto, da kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso sun halarci taron kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar Peoples Democratic Party a Abuja.

KU KARANTA KUMA: Kotun Kaduna ta sanya ranar 4 ga watan Oktoba don yanke hukunci kan belin Zakzaky

Tsohon shugaban jam’iyyar, Cif Barnabas Gemade da kuma jakadan Najeriya a kasar Afrika ta kudu, Alhaji Ahmed Ibeto suma sun hallara a wajen taron.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel