Kotu ta bayar da belin kanin matar Obasanjo

Kotu ta bayar da belin kanin matar Obasanjo

- Bayan karbar gabza a kurkuku na mako guda kotu ta bayar da belin surikin Obasanjo

- Tun a makon da ya gaba ta ne EFCC ta gurfanar da shi gaban alkali a Legas amma gaza cika sharuddan beli ya sanya shi tafiya gidan yari

Kotun laifuffuka na musamman dake Ikeja a jihar Legas ta bayar da belin wani hamshakin dan kasuwa bisa laifin yin takardun jabu.

Kotu ta bayar da belin kanin matar Obasanjo

Kotu ta bayar da belin kanin matar Obasanjo

Mai Shari'a Mojisola Dada ta bayar da umarnin sakin Abebe wanda kani ne ga mai dakin shugaban kasa wato Stella Obasanjo, biyo bayan bukatar belin da ya gabatar mata.

KU KARANTA: EFCC ta biyo ta kan kanin matar Obasanjo

Idan za'a iya tunawa dai a ranar 26 ga watan Yuli ne hukumar EFCC ta cafke Mista Ababe bisa laifin yin takardun jabu.

Har kawo yau dai an ajiye shi a gidan yarin Ikoyi, sai da lauyansa Uche Nwokedi (SAN) ya gabatar da sharuddan belin ga kotun wanda ta bukata.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel