Yanzu Yanzu: Shugabannin kananan hukumomi, kansiloli sun sauya sheka daga APC zuwa PDP

Yanzu Yanzu: Shugabannin kananan hukumomi, kansiloli sun sauya sheka daga APC zuwa PDP

Shugabannin kananan hukumomi da kansiloli a jihar Kwara sun sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress zuwa Peoples Democratic Party.

Shugaban kungiyar kanananan hukumomin Najeriya, babin jihar Kwara, Mista Joshua Omokanye, yace dukannin shugabannin kananan hukumomi 16 da dukkanin kansilolin da aka zaba karkashin APC sun sauya sheka zuwa PDP.

Yanzu Yanzu: Shugabannin kananan hukumomi, kansiloli sun sauya sheka daga APC zuwa PDP

Yanzu Yanzu: Shugabannin kananan hukumomi, kansiloli sun sauya sheka daga APC zuwa PDP

Yayi Magana yayinda yake zantawa da manema labarai kan sauya shekar a ranar Alhamis, 2 ga watan Agusta a Ilorin, babban birnin jihar Kwara.

KU KARANTA KUMA: Nasarar Buhari a zaben 2019 wajibi ne - Maharaji

A halin da ake ciki, Shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Rochas Okorocha ya ba da tabbacin cewa babu wani gwamna da zai sake sauya sheka daga jam’iyyar.

Gwamnan ya ba da tabbacin ne a karshen ganawar sirrin da suka yi tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin na APC a fadar shugaban kasa a daren ranar Laraba.

Okorocha wadda ya sanar da manema labarai na fadar shugaban kasa abunda ganawar tasu ta kunsa ya bayyana cewa sun tattauna akan sauya shekar biyu daga cikin takwarorinsu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel