Babu gwamnan da zai sake barin APC – Okorocha ya tabbatarwa da Buhari

Babu gwamnan da zai sake barin APC – Okorocha ya tabbatarwa da Buhari

Shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Rochas Okorocha ya ba da tabbacin cewa babu wani gwamna da zai sake sauya sheka daga jam’iyyar.

Gwamnan ya ba da tabbacin ne a karshen ganawar sirrin da suka yi tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin na APC a fadar shugaban kasa a daren ranar Laraba.

Okorocha wadda ya sanar da manema labarai na fadar shugaban kasa abunda ganawar tasu ta kunsa ya bayyana cewa sun tattauna akan sauya shekar biyu daga cikin takwarorinsu.

Babu gwamnan da zai sake barin APC – Okorocha ya tabbatarwa da Buhari

Babu gwamnan da zai sake barin APC – Okorocha ya tabbatarwa da Buhari

Ya kuma bayyana cewa shugaban kasa Buhari na nufin kasar da alkhairi ba sharri ba.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa na ajiye mukamina na jakadan Najeriya a Afrika ta kudu na koma PDP - Ibeto

Gwamnan ya kuma jadadda cewa a yanzu suna da jihohi 22 da kuma sanatoci 53. Cewa babu wadda zai sake barin jam’iyyar a nan gaba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel