Ndume, Adamu, Omo-Agege na kulla makirci don tsige Saraki – Yan majalisa na PDP

Ndume, Adamu, Omo-Agege na kulla makirci don tsige Saraki – Yan majalisa na PDP

Wasu mambobin majalisar dattawa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party saunyi zargin wani ana shirya wata makarkashiya domin tsige Saraki.

Yan majalisan sun ambaci sunayen Sanata Ali Ndume, Sanata Abdullahi Adamu da Sanata Ovie Omo-Agege a matsayin wadanda ke shirya makarkashiyar.

Mambobin majalisan sun bayyana an gano santocin uku da maraicen ranar Laraba a majalisar dattawa, da zargin cewa zasu balle kofa zuwa zauren majalisar.

Ndume, Adamu, Omo-Agege na kulla makirci don tsige Saraki – Dan majalisa na PDP

Ndume, Adamu, Omo-Agege na kulla makirci don tsige Saraki – Dan majalisa na PDP

An tattaro cewa sajan dake kula da majalisar ya hana su shiga ta hanyar rufe kofofin majalisar da kacha.

Shugaban masu rinjaye a majalisa, Mista Chukwuka Onyema, wadda yayi Magana da manema labarai a majalisar dokokin kasar ya bayyana cewa mambobin sun samu labara sannan suka yi gaggawan zuwa majalisar dattawan domin ceto damokradiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel