Rayukan Mutane 5 sun salwanta cikin wani hargitsi a jihar Filato

Rayukan Mutane 5 sun salwanta cikin wani hargitsi a jihar Filato

Hukumar 'yan sanda reshen jihar Filato, ta bayar da tabbacin salwantar rayukan mutane biyar a sanadiyar wani hargitsi da ya auku tsakanin kungiyoyin asiri a babban birnin jihar na Jos.

Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, Mista Terna Tyopev, shine ya bayar da shaidar hakan yayin ganawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya a ranar Larabar da ta gabata dangane da aukuwar wannan yamutsi a daren ranar Talata.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan lamari ya auku ne a unguwar Rafiki daura da babbar hanyar Rukuba a birnin Jos, inda jami'an tsaro suka yi kacibus da gawar mutane biyar yayin tunkarar lamarin.

Rayukan Mutane 5 sun salwanta cikin wani hargitsi a jihar Filato

Rayukan Mutane 5 sun salwanta cikin wani hargitsi a jihar Filato

Legit.ng ta fahimci cewa, hukumar 'yan sanda ta kuma tsinto kwararon alburusai na bindigar AK 47, muggan kwayoyi na tabar wiwi da kuma kwalaben barasa.

KARANTA KUMA: Dukkanin naɗe-naɗen gwamnatin Buhari mafi tsoka na ga Jihohin Legas da Katsina - Saraki

A yayin ci gaba da binciken diddigi a wannan yankin na tsuburi, hukumar 'yan sanda ta kuma sake kacibus da gawar wani mutum guda, inda tuni aka garzaya da su babbab asibitin koyarwa na Bingham domin killace su a dakunan ajiyar gawa.

Kakakin 'yan sandan ya kara da cewa, tuni dai hukumar ta baza jami'an ta a wannan yankin domin kwantar da tarzoma, inda za ta ci gaba da kai komo domin bankado miyagun da suka aiwatar da wannan aika-aika.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel