Yadda Tambuwal ya ba ni cin hancin Naira miliyan N13m don na bi shi PDP – Dan majalisar

Yadda Tambuwal ya ba ni cin hancin Naira miliyan N13m don na bi shi PDP – Dan majalisar

- Zancen Duniya baya buya ko an binne shi sai ya fito

- Bayan kadawar guguwar sauyin sheka a Najeriya, yanzu haka ta fito fili yadda ake amfani da kudi wajen siyen 'yan majalisu domin sauya sheka

Wani dan Majalisar dokoki daga jihar Sokoto ya tona asirin yadda gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal ya baiwa ‘yan majalisun jihar kudi Naira miliyan 13, gabanin ficewa daga jamiyyar APC a jiya.

Yadda Tambuwal ya ba ni cin hancin Naira miliyan N13m don na bi shi PDP – Dan majalisar

Yadda Tambuwal ya ba ni cin hancin Naira miliyan N13m don na bi shi PDP – Dan majalisar

Dan Majalisar ya kara da cewa shi ya yi watsi da tayin Naira miliyan 13 daga Aminu Tambuwal ne domin ba zai bar jamiyyarsa ta APC zuwa jamiyyar PDP ba.

Ya tabbatar da cewa dukkanin mambobin majalisar jihar 18 da suka bi gwamnan zuwa PDP sun karbi toshiyar bakin ta Naira miliyan 13 kowannesu.

Yadda Tambuwal ya ba ni cin hancin Naira miliyan N13m don na bi shi PDP – Dan majalisar

Yadda Tambuwal ya ba ni cin hancin Naira miliyan N13m don na bi shi PDP – Dan majalisar

Duk dai har ya zuwa yanzu ba’a tabbatar da ikirarin dan majalisar ba, amma dai an san shi yayi kaurin suna waje yin biyayya ga tsohon gwamnan jihar wato Aliyu Wammako.

KU KARANTA: Ni da Kwankwaso ne jagororin PDP a Kano - Shekarau

‘Dan majalisar ya shaida cewa “An yi mana tayin kudi kimanin Naira miliyan 13 ga kowanne mu domin mu shiga jamiyyar PDP, amma ni da sauran mambobin majalisar 11 mun ki karbar wannan kudin".

”Zamu cigaba da zama a cikin jamiyyar APC tare da yin biyayya ga mai-gidanmu Sanata Aliyu Wammako tare da shugabancin Shugaban kasa Muhammad Buhari".

“Babu wata tsoratarwa ko tozarcin siyasa da zai sa mu sauya matsayinmu na zama a cikin jam’iyyar".

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa duk da ficewar gwamnan da wasu ‘yan majalisun zuwa PDP, mataimakin gwamnan Alhaji Ahmed Aliyu har yanzu yana nan cikin jam’iyyar APC.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel