Dalilin da yasa na ajiye mukamina na jakadan Najeriya a Afrika ta kudu na koma PDP - Ibeto

Dalilin da yasa na ajiye mukamina na jakadan Najeriya a Afrika ta kudu na koma PDP - Ibeto

Tsohon jakadan Najeriya a kasar Afrika ta Kudu, Alhaji Ahmed Ibeto, yace ya yanke shawarar komawa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) domin ya samu damar cimma burinsa na inganta jihar Niger da kuma kara mata ayyukan cigaba da bunkasa.

Ibeto, wadda ya kasance mataimaki gwamna a lokacin gwamnatin tsohon gwamna Muazu Babangida Aliyu a jihar, ya fadama taron jama’a a mahaifarsa, jim kadan bayan ya karbi katinsa na dan jam’iyya a PDP No 023, a mazabar Ibelu, a ranar Talata cewa zai kawo tarin kwarewarsa wajen bunkasa jihar.

Dalilin da yasa na ajiye mukamina na jakadan Najeriya a Afrika ta kudu na koma PDP - Ibeto

Dalilin da yasa na ajiye mukamina na jakadan Najeriya a Afrika ta kudu na koma PDP - Ibeto

Ibeto wadda ya ajiye aikinsa na Jakadan Najeriya a kasar Afrika ta Kudu a ranar Litinin da ta gabata yace yana godiya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari har yanzu bisa karamci da yayi na nada sa a matsayin jakada domin ya wakilci Najeriya a Afrika ta Kudu da kuma yadda da yayi das hi a matsayinsa na dan siyasa domin yayiwa kasarsa Najeriya aiki..

KU KRANTA KUMA: Baka isa ka rufe majalisar dattawa kan wasu lamura naka na daban ba – Ndume ya caccaki Saraki

Ibeto ya kai takardar ajiye aiki zuwa ofishin jakadancin Najeriya a ranar Litinin yayinda ya koma PDP, jam’iyyar da ya bari a 2014 gab da shirin zabe na 2015.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel