Jam’iyyar APC ta nada Sakataren yada labarai na rikon kwarya

Jam’iyyar APC ta nada Sakataren yada labarai na rikon kwarya

Mun samu sanarwa cewa Jam’iyyar APC mai mulki ta nada sabon Sakataren yada labarai na rikon kwarya. Hakan na zuwa ne bayan da Bolaji Abdullahi ya tattara ya ajiye mukamin sa a makon nan.

Tsohon Sakataren yada labarai na Jam’iyyar APC Bolaji Abdullahi ya fice daga Jam’iyyar ya kuma ajiye mukamin sa na Sakataren yada labarai inda ya bi tsohon Mai gidan san watau Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki.

Jam’iyyar APC mai mulki ta nada Yekini Nabena wanda shi ne Mataimakin Sakataren yada labarai na Jam’iyyar ya maye gurbin da Bolaji Abdullahi ya bari. Yekini Nabena zai rike wannan mukami ne na rikom kwarya kafin ayi zabe.

KU KARANTA: Sanata Rabiu Kwankwaso ya kai ziyara Jihar Shugaban Kasa

Bolaji Abdullahi dai ya fito ne daga Jihar Kwara kuma ya rike Minista a lokacin mulkin Goodluck Jonathan. Bolaji ya ajiye mukamin sa a lokacin bayan ficewar su Bukola Saraki daga Jam’iyyar PDP ya kuma samu matsayi a APC.

A kwanakin bayan nan ne Jam’iyyar APC mai mulki tayi zaben sababbin shugabanni inda Bolaji Abdullahi ya kara komawa kujerar sa da kuri’u 2002. Bolaji Abdullahi ya doke Abdul Sidiq wanda ya samu kuri’u 243 ya dare kujerar sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel