Muhimman dalilai guda 4 da suka sanya Saraki barin APC

Muhimman dalilai guda 4 da suka sanya Saraki barin APC

Al'amuran siyasar Najeriya sun shiga rudani a karshen wannan watan daya gabata zuwa farkon wannan watan da muke ciki

Muhimman dalilai guda 4 da suka sanya Saraki barin APC

Muhimman dalilai guda 4 da suka sanya Saraki barin APC

Al'amuran siyasar Najeriya sun shiga rudani a karshen wannan watan daya gabata zuwa farkon wannan watan da muke ciki.

Guguwar siyasar Najeriya ta fara kadawa da wasu manya - manyan 'yan siyasar kasar, wadanda suka dinga canja sheka daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki suna komawa babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP).

DUBA WANNAN: Da gangan Saraki ya dinga yiwa jam'iyyar APC zagon kasa - Lai Mohammed

A cikin wadanda guguwar ta dauka harda shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki da mutanen sa, inda suka yi bayanin cewar wasu dalilai ne suka tursasa su barin jam'iyyar. Ga muhimman dalilai guda hudu da Sarakin ya kawo a kasa kamar haka:

1. Mayar da mutanensa saniyar ware

Saraki yace a cikin shakaru ukun da jam'iyyar APC tayi tana mulki, an maida su shida mutanen sa tamkar saniyar ware, ba a yin aikin komai dasu, jam'iyyar ta mai da su tamkar wasu agololi. Sannan kuma yace wasu tsirarun mutane da suke yiwa gwamnati juyin waina, sun hana duk wata kofa da za abi domin warware matsalolin jam'iyyar.

2. 'Yan hana ruwa gudu

A bayanin da shugaban majalisar dattawan yayi Sanata Bukola Saraki, yace akwai wasu 'yan kaudi a jam'iyyar APC da suke toshe duk wata kafa da za'a iya amfani da ita wurin gabatar da sulhu da kuma tabbatar da zaman lafiya a jam'iyyar.

Saraki yayi zargin cewa mutanen sunyi watsi da duk wasu dokoki na jam'iyyar APC wadanda zasu saka a samu dai dai to a cikin jam'iyyar.

3. Batawa 'yan majalisa suna a idon al'umma

Saraki yace duk irin namijin kokarin da yake yi wajen baiwa gwamnatin APC kariya a majalisun kasa a matsayin sa na shugaban majalisa, bangaren zartarwa na yiwa duk wani mataki nasu zagon kasa. Yace ba sau daya ba an sha yin amfani da ikirarin da gwamnatin tarayya ke yi na yaki da cin hanci da rashawa a bata musu suna.

4. Tura ta kai bango

Saraki yace daya daga cikin manyan dalilan da suka saka shi barin jam'iyyar ta APC shine, ganin yanda wasu manya daga cikin jam'iyyar suke yiwa duk wani yunkuri na ganin sunyi watsi da duk wani kokari da suke na gabatar da sulhu a jam'iyyar musamman ma a kwana-kwanan nan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel