Aikin gwamnatin Buhari: An fara gudanar da katafaren aikin jirgin kasa sabo

Aikin gwamnatin Buhari: An fara gudanar da katafaren aikin jirgin kasa sabo

- Gwamantin tarayya ta himmatu da cigaba da kera titunan jiragen kasa a fadin kasar nan

- Bayan samun cikas yayin fara aikin ginin titin a jihar Legas, yanzu haka an shawo kan matsalar

- Ministan sufuri na kasa Rotimi Ameachi ya tabbatar da cewa nan da lokaci kadan za'a kai ga gaci

Hukumar kula da harkokin jiragen kasa wato NRC ta bayyana cewa aikin layin dogo daga jihar Legas zuwa Ibadan ya kankama, sakamakon shawo kan matsalar da aka ci karo da ita.

Aikin gwamnatin Buhari: An fara gudanar da katafaren aikin jirgin kasa sabo

Aikin gwamnatin Buhari: An fara gudanar da katafaren aikin jirgin kasa sabo

Babban jami'in hukumar mai kula da shiyyar Legas Mista Jerry Oche ne ya bayyanawa kamfanin dillanci labarai na kasa (NAN), cewar an fara shimfida titin dogo daga Legas zuwa Ibadan.

“Kamar yadda muka tabbatar da ingancin titin dogo da ya tashi daga Apapa a jihar Legas zuwa Ijoko da ke jihar Ogun, haka wanda ya tashi daga Legas zuwa Ibadan zai kasance". In ji Jerry Oche.

KU KARANTA: ‘Yan Boko Haram sun ga ta kansu: Sojin saman kasar nan ta yi musu barin wuta (Bidiyo)

"Hakika gwamnatin tarayyar kasar nan da gaske ta ke akan batun titin dogo, domin tana bayar da hadin kai yadda ya kamata wanda hakan ya haifar da cigaban aikin a shiyyar Legas".

Da farko bayan fara aikin an fuskanci matsalar gamuwa da bututan ruwa da na wayoyin lantarki a cikin Legas, wanda hakan ya kawo tsaikon fara aikin.

A nasa bangaren ministan harkokin sufuri na kasa Rotimi Amaechi ya bayyana cewa rashin fara aikin akan kari na da nasaba da matsalar wasu ababen da al'umma ke amfani da su. ministan ya bayyana hakan ne a tashar jirgin kasa dake Papalanto a jihar Ogun.

"Na gamsu da yadda ake tafiyar da aikin dogon, wanda nan da wani dan lokaci za'a kai ga nasarar abin da ake bukata" Amaechi ya tabatar.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel