Farfesa Hafiz ya karyata batun yin murabus daga mukamin mataimakin Ganduje

Farfesa Hafiz ya karyata batun yin murabus daga mukamin mataimakin Ganduje

Mataimakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar ya karyata rahoton dake yawo a shafukan yanar gizo na cewa wai ya yi murabus daga mukamin mataimakin gwamnan jihar Kano, bayan ficewa daga APC zuwa PDP inji rahoton jaridar Daily Nigerian.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Hafiz, wanda aminin tsohon gwmnan jihar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne, ya musanta rahoton ajiye aiki, inda yace yana nan akan mukaminsa, don ko a yanzu yana bakin aikinsa.

KU KARANTA: Shehu Sani a neman kariyar Allah daga sharrin masharranta da hassadan mahassada

“Ban yi murabus ba, har yanzu nine mataimakin gwamnan jihar Kano, a yanzu haka ina garin Abuja na halarci wani taro na hukumar ilimi ta kasa.” Inji shi, sai dai Farfesan yace zai yanke shawara game da makoma siyasarsa nan bada jimawa ba.

Farfesa Hafiz ya karyata batun yin murabus daga mukamin mataimakin Ganduje

Farfesa Hafiz

Farfesan yace: “Zan yanke shawara dangane da makomar siyasata a lokacin da ya dace bayan na tattauna da shuwagabannina a siyasance.” Sa’annan ya zargi wasu mutane dage cikin gwamnatin Ganduje da yada wannan jita jita.

Idan za’a tuna, a ranar Talata, 2 ga watan Agusta ne Hafiz ya aika ma hukumar tsaro ta sirri, DSS, korafin cewa rayuwarsa na cikin hadari sakamakon barazana da ake yi masa, tare da wata makarkashiya da gwamnatin jihar ke shirya masa.

Sai dai ana ganin kasancewar Hafiz na hannun daman Kwankwaso ne yana iya zama dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, idan har ya sauya sheka zuwa jam’iyyar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel