Buhari ya tubure sai Saraki ya sauka daga mukamin shugaban majalisar Dattawa

Buhari ya tubure sai Saraki ya sauka daga mukamin shugaban majalisar Dattawa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari y adage kai da fata lallai sai shugaban majalisar dattawa, Sanata Abubakar Bukola Saraki ya sauka daga mukamin shugabancin majalisa tunda dai ya sauya sheka daga jam’iyya mai rinjaye a majalisar, APC, zuwa jam’iyya mara rinjaye.

Legit.ng ta ruwaito shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomole ne ya bayyana haka bayan wata ganawar sirri da yayi da shugaba Buhari tare da sanatocin jam’iyyar APC gaba daya a fadar gwamnati dake Abuja, inda yace kamata yayi tunda girma da arziki Saraki ya yi murabus.

KU KARANTA: Yadda wasu yan majalisa Mata suka baiwa hammata iska saboda Namiji

“Abinda yafi dacewa ga duk mutum mai mutunci a irin wannan hali shine ya yi murabus, ma’ana bai kamata ka dauki abinda yake mallakinka bane, don ko a haka APC c eke da rinjaye a majalisa, muna Sanatoci 53, sama da na PDP da APGA.” Inji shi.

Adams ya cigaba da cewa: “Duk dan APC ba zai yi mamakin abinda ke faruwa ba, watakila ma sun yi lattin fita, muna cikin tsaka mai wuya, amma dadin abin shine, duk girmanka duk kankantanka, kuri’arka guda daya ce.”

Haka zalika Oshiomole ya bayyana jin dadinsa da yadda Saraki da kansa ya tabbatar da irin kokarin da mataimakin shugaban kasa Osinbajo da na shi kansa Oshiomole suka yi wajen shawo kan matsalar.

Daga karshe Adams yace akwai darussan koya daga wadannan lamurra dake faruwa a jam’iyyar APC a yanzu, don haka yace yana fatan jam’iyyar zata kara karfi anan gaba kadan ta hanyar gyara duk matsalolin da suke fama dasu a yanzu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel