Dukkanin naɗe-naɗen gwamnatin Buhari mafi tsoka na ga Jihohin Legas da Katsina - Saraki

Dukkanin naɗe-naɗen gwamnatin Buhari mafi tsoka na ga Jihohin Legas da Katsina - Saraki

Shugaban Majalisar dattawa a ranar Talatar da ta gabata ya gana da magoya bayan sa cikin birnin Ilorin, inda ya zayyana ma su dalilin sa na ficewa daga jam'iyyar APC sakamakon da'awar su akan aikata hakan da kuma jibintar lamarin sa da Mai Duka ya yi.

Saraki dai ya bayyana cewa, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari karkashin inuwa ta jam'iyyar APC ta maishe da jihar sa ta Kwara saniyar ware musamman a bangaren naɗe-naɗen mukamai.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, Saraki ya bayyana hakan ga manema labarai bayan ganawar sa da gwamnan jihar, 'yan majalisar ta na dokoki da na tarayya, shugabannin kananan hukumomi da kuma jiga-jigan gwamnatin jihar.

Dukkanin naɗe-naɗen gwamnatin Buhari mafi tsoka na ga Jihohin Legas da Katsina - Saraki

Dukkanin naɗe-naɗen gwamnatin Buhari mafi tsoka na ga Jihohin Legas da Katsina - Saraki

Saraki yake cewa, gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Buhari ta aiwatar da naɗe-naɗen ta mafi tsoka ga mutane daban-daban fiye da 200 da suka fito daga jihohin Legas da kuma Katsina.

Ya ci gaba da cewa, gwamnatin Buhari ta maishe da jihar sa ta Kwara da kuma ta Kakakin majalisar wakilai saniyar ware ta bangaren gudanar da naɗe-naɗen ta mafi tsoka, wanda hakan ya tabbatar da rashin bukatar sa da gwamnatin ke yi a jam'iyyar.

KARANTA KUMA: Aisha Buhari ta tafi 'Kasar Burkina Faso domin yawon wayar da kai kan yaki da Cutar Daji

Shugaban majalisar ya kara da cewa, sun koma jam'iyyar PDP ne da yakinin samun dama ta kwankwadar romon dimokuradiyya.

A yayin haka kuma jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a daren jiya na Laraba shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da ragowar sanatocin jam'iyyar APC a fadar sa ta Villa dake babban birnin kasar nan na tarayya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel