Ficewar Saraki daga jam’iyyar APC tamkar mutuwar jam’iyyar ne ― Balarabe Musa

Ficewar Saraki daga jam’iyyar APC tamkar mutuwar jam’iyyar ne ― Balarabe Musa

- Duk da cewa APC ta bayyan cewa ko a jikinta ficewar shugaban majalisar dattijai, amma da alama wasu na ganin zancen akwai sake

- Balarabe Musa ya bayyana cewa rashin Saraki da APC tayi tamkar ta rasa numfashinta ne

- Bukola Saraki dai shi ma ya shiga cikin guguwar sayin shekar da ta kada daga APC zuwa PDP

Tsohon gwamnan jihar Kaduna Alhaji Balarabe Musa ya bayyana cewa ficewar shugaban majalisar dattawa Dakta Abubakar Bukola Saraki daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP zai kawo nakasu ga nasarar shugaba Muhamm ad Buhari a kakar zaben shekarar 2019.

Ficewar Saraki daga jam’iyyar APC tamkar mutuwar jam’iyyar ne ― Balarabe Musa

Balarabe Musa

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wata ganawa da ya yi da manema labarai a jiya Talata, inda ya jaddada cewa babu shakka ficewar Sarakin za ta kawo tangarda tare da kawo cikas ga shugaba Muhammad Buhari tare da jam’iyyarsa ta APC a zaben 2019.

Idan za'a iya tunawa dai a ranar Talata ne dai shugaban majalisar dattawan ya fice daga jamiyyar APC zuwa jam’iyyar PDP.

KU KARANTA: Ko a jikinmu ficewar Bukola Saraki - Lai Mohammed

"Ficewar Bukola Saraki daga jam’iyyar APC ya sanya jam’iyyar cikin rudani, domin kai tsaye karshen jam’iyyar ya zo". A cewar Balarabe Musa.

Sannan ya kara da "Babu Shakka abubuwan da za su biyo baya bayan ficewar Saraki daga jam’iyyar APC, ba zai haifarwa da jam’iyyar da mai ido ba. Domin zai kawo cikas ga nasarar jam’iyyar a zabe mai zuwa".

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel