Hukumar 'Yan sanda ta bukaci 'yan siyasa a Jihar Kano da su guje wa tayar da tarzoma da kalaman nuna ƙiyayya

Hukumar 'Yan sanda ta bukaci 'yan siyasa a Jihar Kano da su guje wa tayar da tarzoma da kalaman nuna ƙiyayya

Hukumar 'yan sanda reshen jihar Kano, ta gargadi mazauna jihar musamman 'yan siyasa akan kauracewa tayar da tarzoma da kuma kalaman nuna kiyayya a yayin da babban zabe na 2019 ke ci ga da karatowa.

Kakakin hukumar na jihar, SP Magaji Musa Majiya, shine yayi wannan kira yayin ganawa da manema labarai cikin Birnin Dabo a ranar Larabar da ta gabata.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, hukumar ta yi wannan gargadi gami da jan kunne sakamakon yadda wasu al'ummar jihar ke tarwatsa fastoci da kuma ababen tallata shugaba Buhari daura da hanyar Sharada a cikin tantagwaryar birnin Kano.

DSP Magaji Musa Majiya

DSP Magaji Musa Majiya

Ya kuma gargadi 'yan siyasa kan kauracewa furta kalaman nuna kiyayya ga abokanan adawar su yayin yakin neman zabe da ya sabawa ka'ida ta dimokuradiyya.

Majiya ya ci gaba da cewa, hukumar ta tanadi jami'ai domin sanya idanun lura tare da damukar duk masu yunkurin tayar da tarzoma da manufa ta adawar siyasa.

KARANTA KUMA: Gwamna Masari ya caccaki Shugabannin Arewa akan al'amurran da suka shafi Ilimi

Kakakin ya kuma nemi iyaye da dukkanin wadanda ke da alhakin kulawar wasu a karkashin su akan su sanya idanun lura a kansu domin gudun amfani da su a matsayin 'yan bangar siyasa.

Majiya ya kuma nemi al'ummar jihar akan hada gwiwa da hukumomin tsaro wajen shigar da rahoton duk wani abun rashin yarda da suka hanga, inda ya bayar da lambobin wayar tarho da za rika tuntubar su cikin gaggawa kamar haka: 08032419754; 08123821575.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel