Ko a jikinmu ficewar Bukola Saraki - Lai Mohammed

Ko a jikinmu ficewar Bukola Saraki - Lai Mohammed

- Bukola Saraki yana sane yake sanya cigaban gwamnatin Buhari take yin tafiyar Hawainiya

- Don haka ficewarsa ba zata ragewa APC komai ba a zaben 2019

Ministan yada labarai da al'adu na kasa Alhaji Lai Mohammed ya bayyana cewa ficewar shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki daga Jamiyyar APC ba zai kawo nakasu ga nasarar jam’iyyar a kakar zaben Shekarar 2019.

Ko a jikinmu ficewar Bukola Saraki - Lai Mohammed

Ko a jikinmu ficewar Bukola Saraki - Lai Mohammed

Ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a yau Laraba a birnin tarayya Abuja. Sanarwar ta kara da cewa zaman Saraki a cikin jam’iyyar ta APC bai amfani jam’iyyar da komai ba.

KU KARANTA: Ka shirya tattara kayanka, zamu tashi kiyamar siyasarka a 2019 – APC ga wani Sanatan Arewa

”Idan da a ce shugaban Majalisar dattawa ba dan jam’iyyar APC ba ne, to babu shakka jam’iyyar APC ba za ta fuskanci matsalolin da ta fuskanta ba a zauren majalisar dattawa ba, domin ta fuskanci matsalolin jinkirin aiwatar da kasafin kudi tare da kin amincewa da nada manyan mukamai a cikin kunshin gwamnatin APC " in ji Lai Mohammed.

Ya kara da cewa "Ya dade yana zagon kasa ga jam’iyyarmu Ramlat Dan adawa, yana sane ya ke kawo cikas gami da jan kafa wajen aiwatar da dukkanin abin da zai kawo cigaban kasar nan, saboda haka jam’iyyar APC ba ta yi asarar ficewarsa ba".

Daga nan ne ya tabbatar da cewa jam’iyyar APC a jihar Kwara tana nan da tasirinta, domin ba tayi wani babban gibi ba.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel