Tsohon Gwamnan Kano Kwankwaso ya leka Katsina ziyarar ta’aziyya da jaje

Tsohon Gwamnan Kano Kwankwaso ya leka Katsina ziyarar ta’aziyya da jaje

- Sanata Kwankwaso ya kai ziyara har Mahaifar Shugaban kasa Buhari

- ‘Dan Majalisar ya jajantawa wadanda musiba ta auka masu a kwanaki

- Tsohon Gwamnan na Kano ya kuma yi ta’aziyya na wani rashi da aka yi

Sanatan Kano ta tsakiya Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyara Jihar Katsina a yau dinnan inda yayi ta’aziyya ga Iyalan Marigayi tsohon Sufeta Janar na ‘Yan Sandan Najeriya Ibrahim Commassie sannan kuma yayi jaje a Garin Jibiya.

Tsohon Gwamnan Kano Kwankwaso ya leka Katsina ziyarar ta’aziyya da jaje

Sanata Kwankwaso ya kai ziyara gidan Marigayi Commassie

Marigayi Sardaunan Katsina Ibrahim Commassie ya rasu ne kwanaki inda Sanatan na Jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso yayi wa Iyalan na sa da Katsinawa ta’aziyya. Commassie ya rike Shugaban ‘Yan Sanda a lokacin mulkin Soji.

KU KARANTA: Gwamnan Katsina ya caccaki Shugabannin Arewa kan harkar ilmi

Sanatan na Kano ne ya bayyana wannan ta shafin sa na Tuwita watau @KwankwasoRM. Bayan nan kuma mun ji labari cewa Tsohon Gwamnan ya leka cikin Garin Jibiya inda ya jajantawa wadanda musiba ta aukawa kwanakin baya.

‘Dan Majalisar ya jajantawa wadanda ruwan daminan bana yayi masu gyara. Sanatan ya rabawa Bayin Allah buhunan shinkafa 400. Bayan nan dai Sanatan ya kama hanya ya koma gida inda jama’a su ka rika daga masa hannu.

Kun ji labari dazu cewa Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar, ya bi Kwankwaso bayan ya sauya sheka daga jam'iyyar All Progressives Congress APC zuwa jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel