Shugaban majalisa, mambobi 17 na majalisar dokokin jihar Sokoto sun fita daga APC

Shugaban majalisa, mambobi 17 na majalisar dokokin jihar Sokoto sun fita daga APC

Shugaban majalisar dokokin jihar Sokoto, Alhaji Salihu Maidaji, da wasu mambobin majalisar 17 sun fita daga jam’iyyar APC tare da tsallakawa zuwa jam’iyyar PDP.

Mu, mambobi 18 na majalisar dokokin jihar Sokoto mun saka hannu tare da bayyana biyayyar mu ga tsagin APC da Alhaji Buba Galadima ke jagoranta,” Maidaji ya sanar yayin zaman majalisar nay au, Laraba.

Maidaji ya kara da cewa suna sane da irin kokarin da APC tayi na dinke barakar dake tsakanin ‘ya’yanta amma hakan bai yiwu ba, a saboda haka cigabansu da zama a jam’iyyar hatsari ne, kamar yadda ya bayyana.

Shugaban majalisa, mambobi 17 na majalisar dokokin jihar Sokoto sun fita daga APC

Tambuwal yayin sanar da fita daga APC

Shugaban majalisar ya bayyana cewar sun koma jam’iyyar PDP kamar yadda sashe na 109(1) da aka yiwa kwaskwarima ya basu dama.

DUBA WANNAN: Abinda fitar Saraki daga APC ke nufi ga jam'iyyar - Farfesa Sagay

Da yake magana a kan canjin Maidaji da ragowar mambobin majalisar, Alhaji Sani Yakubu, jagoran mambobin majalisar 12 da suka yanke shawarar cigaba da zama a APC, y ace “muna yi masu fatan alheri a sabuwar jam’iyyar da suka shiga.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel