'Yan majalisar Tambuwal 12 sunki binshi PDP, sun nuna goyon bayan su ga shugaba Buhari

'Yan majalisar Tambuwal 12 sunki binshi PDP, sun nuna goyon bayan su ga shugaba Buhari

- A yau ne gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya canja sheka daga jam'iyyar APC mai mulki zuwa babbar jam'iyyar adawa ta PDP

- Sai dai kuma da yawa daga cikin 'yan majalisar jihar sunki nuna goyon bayan su gareshi, inda suka bayyana cewar suna tare da shugaba Buhari dari bisa dari

'Yan majalisar Tambuwal 12 sunki binshi PDP, sun nuna goyon bayan su ga shugaba Buhari

'Yan majalisar Tambuwal 12 sunki binshi PDP, sun nuna goyon bayan su ga shugaba Buhari

'Yan majalisu 12 daga cikin 'yan majalisu 30 na jihar Sokoto sun nuna goyon bayansu dari bisa dari ga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari. 'Yan majalisun sun bayyanawa manema labarai hakan a yau Larabar nan.

DUBA WANNAN: Shehu Sani ya bayyana hanyoyi biyar da gwamnatin Buhari zata tafi da wadanda suka bar jam'iyyar APC

Sanarwar ta su ta biyo bayan canja shekar da gwamnan jihar Aminu Tambuwal yayi zuwa babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) daga jam'iyya mai mulki ta All Progressives Party (APC).

A lokacin da yake sanar da fitar shi daga jam'iyyar a yau Larabar nan, gwamnan ya zargi gwamnatin shugaba Buhari a matsayin wacce ta kasa cika alkawuran data dauka.

'Yan majalisun sun zargi gwamnan da neman kujerar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP, wanda ya samu goyon bayan 'yan majalisun sa su 18.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel